Gunduma ta 9 na Paris | |||||
---|---|---|---|---|---|
| |||||
| |||||
Wuri | |||||
| |||||
Ƴantacciyar ƙasa | Faransa | ||||
Administrative territorial entity of France (en) | Metropolitan France (en) | ||||
Region of France (en) | Île-de-France (en) | ||||
Department of France (en) | Seine (en) | ||||
Territorial collectivity of France with special status (en) | Faris | ||||
Yawan mutane | |||||
Faɗi | 58,951 (2021) | ||||
• Yawan mutane | 27,041.74 mazaunan/km² | ||||
Labarin ƙasa | |||||
Yawan fili | 2.18 km² | ||||
Sun raba iyaka da | |||||
Bayanan tarihi | |||||
Mabiyi | former 1st arrondissement of Paris (en) , former 2nd arrondissement of Paris (en) da former 3rd arrondissement of Paris (en) | ||||
Ƙirƙira | 1860 | ||||
Tsarin Siyasa | |||||
• Gwamna | Delphine Bürkli (en) (2014) | ||||
Bayanan Tuntuɓa | |||||
Lambar aika saƙo | 75009 | ||||
Wasu abun | |||||
| |||||
Yanar gizo | mairie09.paris.fr | ||||
Gunduma ta 9 na Paris ( IX e arrondissement ) tana ɗaya daga cikin gundumomi 20 na babban birnin Faransa. Ana kiran wannan yanki da neuvième ( ; "na tara") a harshen Faransanci.
Gundumar wanda ake kira da Opéra, na nan a gefen dama ga Kogin Seine. Ta ƙunshi wurare daban daban na al'adu, tarihi, da wuraren fasaha, ciki har da Palais Garnier, gida ga Paris Opera, Boulevard Haussmann, da kuma manyan ɗakunan ajiya na Galeries Lafayette da Printemps. Wurin yana dauke da gidajen wasan kwaikwayo da dama wanda suka haɗa da Folie Bergères, Théatre Mogador da Théatre de Paris. Tare da sauran gundumomi na 2 da na 8, suna kaddamar da cibiyar kasuwanci na Paris, dake kusa da Opéra .
Fadin ƙasar wannan yanki ya kai kimanin murabba'i 2.179 km2 (0.841 sq. miles, ko 538 acres).
Kungiyar Wikimedia Faransa na da ofisoshinta a cikin unguwar, a 28 rue de Londres.
Groupe Danone na da babban ofishinta a cikin ginin Boulevard Haussmann na 17 a cikin wannan gunduma ta tara. Danone sun koma can acikin shekara ta 2002.
BNP Paribas na da babban ofishinta a cikin gunduma. Crédit Industriel et Commercial . Har wayau Kroll Inc. itama na da ofishi a wannan yanki.
DotEmu na da babban ofishinta a cikin gunduma ta 9.
Gameloft na da ofishi mai rijista da kuma babban ofishinta a cikin wannan gunduma ta 9. Tana nan a kan bene na biyar na 14 rue Auber.
Har zuwa Yuni 1995, babban ofishin Société Générale na nan acikin wannan yanki. A wannan watan babban ofishin ya koma Société Générale Towers . Tsohon babban ofishin ya kasance a matsayin ofishin rajista na kamfanin .
Google Paris itama tana da ofisoshinta a cikin wannan gunduma.
Mafi yawan jama'a a wannan gundumomi ta 9 ya faru ne a cikin shekarar 1901, lokacin da take da mazauna 124,011. Tun daga wannan lokacin, gundumar ta jawo harkokin kasuwanci sosai a yankin. A sakamakon haka, yawan mazauna yankin sun kasance a cikin shekarar 1999 mutum 55,838 ne kacal, yayin da ma'aikata sun kai kimanin mutum 111,939.
Shekara (na ƙidayar Faransa) |
Yawan jama'a | Yawan yawa (mazauna dangane da km2 ) |
---|---|---|
1872 | 103,767 | 47,600 |
1901 (peak of population) | 124,011 | 56,912 |
1954 | 102,287 | 46,921 |
1962 | 94,094 | 43,182 |
1968 | 84,969 | 38,994 |
1975 | 70,270 | 32,249 |
1982 | 64,134 | 29,433 |
1990 | 58,019 | 26,626 |
1999 | 55,838 | 25,626 |
2009 | 60,275 | 27,649 |
}}
79 rue du Faubourg Poissonnière 75009, Paris, France
Wikimedia Commons on Gunduma ta 9 na Paris